(ABNA24.com) Gwamnatin kasar Iran ta sanar da cewa bayan kammala dukkanin bincike daga ma’aikatar shar’ar kasar, an yake hukuncin sakin jirgin ruwan Birtaniya da Iran ta tsare bayan ya sabawa ka’ida zirga-zirgar jiragen ruwan a tekun fasha.
Kakakin gwamnatin kasar ta Iran Ali Rubai’i ne ya sanar da hakan a yau, inda ya ce duk da cewa jirgin na Birtaniya ya sabawa dokoki da ka’idoji na harkokin zirga-zirgar jiragen ruwa a cikin tekun fasha, amma daga karshe ma’aikatar shari’a ta bayar da umarnin cewa zai iya tafiya.
Tun aranar 19 ga watan Yulin da ya gabata ne dai dakarun Iran suka kame katafaren jirgin ruwan dakon mai na kasar Birtaniya a cikin tekun fasha, bayan da ya kashe fitilunsa da kuma tsarin na’urar fayyace taswira na GPS.
Dangane da batun tafiyar shugaba Rauhani zuwa kasar Amurka domin halartar babban taron majalisar dinkin duniya kuwa, Rabi’i ya bayyana cewa, Amurka ta saka siyasa a cikin lamarin bayar da izinin shiga kasar, wanda hakan yasa shugaba Rauhani yin tababa kan tafiyar, amma daga karshe ya yanke shawarar yin tafiyar domin bayyana wa duniya gaskiyar abin da ke faruwa a gabas tsakiya, wanda kuma a cewarsa Amurka ce ta haifar da dukkanin matsaloli a yankin.
/129
24 Satumba 2019 - 04:32
Lambar labari: 977605
Gwamnatin kasar Iran ta sanar da cewa bayan kammala dukkanin bincike daga ma’aikatar shar’ar kasar, an yake hukuncin sakin jirgin ruwan Birtaniya da Iran ta tsare bayan ya sabawa ka’ida zirga-zirgar jiragen ruwan a tekun fasha.